Haruna Lukman ya koma Dynamo Kiev

lukman Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lukman Haruna

Dan kwallon Najeriya Lukman Haruna ya kulla yarjejeniya da kungiyar Dynamo Kiev ta Ukraine akan pan miliyan biyu da dubu dari takwas daga AS Monaco.

Ya koma Monaco ne a shekara ta 2007 jim kadan bayan ya ratayawa Najeriya kyaftin ta lashe gasar cin kofin duniya na 'yan kasada shekaru 17 a Koriya ta Kudu.

Dan kwallon mai shekaru ashirin da daya na cikin tawagar 'yan wasan Super Eagles a Afrika ta Kudu inda ya buga wasan Najeriya tsakaninta da Argentina da kuma Girka.

Monaco dai ta koma rukuni na biyu a gasar kwallon Faransa.

Kafin ya sanya hannu a sabuwar kwangilar a Ukraine, wasu kulob daga Ingila da Faransa sun nuna sha'awa akanshi.