Villas-Boas zai taka rawar gani- In ji Simoes

Villas-Boas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Villas-Boas ya maye gurbin Carlo Ancelotti

Mutumin da ya fara nada Andre Villas-Boas a matsayin koci shugaban Academica Eduardo Simoes ya ce babu shakka sabon kocin na Chelsea zai taka rawar gani.

Shugaban kulob din Academica Jose Eduardo Simoes shi ne ya nada Villas-Boas a matsayin koci a watan Oktoban 2009.

Simoes ya sahida wa BBC cewa: "Zan iya fada kai tsaye cewa bayan haduwata ta farko da shi, na fahimci cewa mutum ne na kwarai, kuma ya cancani shugabanci.

"Zai taka rawar gani a Chelsea kuma nan da shekaru biyu ina saran zai lashe gasar Premier da ta zakarun Turai."

Villas-Boas mai shekaru 33, ya shafe shekaru bakwai yana aiki tare da Jose Mourinho a FC Porto da Chelsea da Inter Milan.

Kafin daga bisani ya koma Academica inda ya tserar da su daga fadawa rukuni na biyu a gasar kwallon Portugal.

Daga nan ne kuma ya koma Porto inda ya lashe kofuna hudu a kaka ta farko da ya shafe a matsayin koci.