Hamayyar Barca da Real Madrid na damu na-Bosque

boque
Image caption Vicente del Bosque

Kocin Spain Vicente del Bosque ya bayyana cewar hammaya tsakanin 'yan wasan Barcelona dana Real Madrid na janyo abu mara kyau a tawagar 'yan kwallon kasar.

Manyan kungiyoyin biyu na La Liga a kakar wasan data wuce sun samu matsala da juna, inda a wasan gasar zakarun Turai aka dakatar da kocin Real Jose Mourinho sannan aka kori golan Barca Jose Pinto.

Del Bosque wanda ke jagorantar tawagar Spain tun shekara ta 2008 ya ce dole ne yayi aiki tukuru don ganin an samu fahimtar juna tsakanin 'yan kwallon kasar.

Yace"dole ne sai mun dinke barakar dake tsakanin 'yan Barcelona da Real Madrid".

Daga cikin 'yan kwallon goma sha daya da suka buga wasan karshe na gasar kofin duniya da Spain ta doke Netherlands, Joan Capdevilla ne kadai baya bugawa Barca ko Real Madrid.

Spain zata buga wasa a nan gaba tsakaninta da Italiya a ranar 10 ga watan Agusta.