Faransa ta doke Najeriya a kwallon mata

falcons
Image caption Super Falcons na Najeriya

Tawagar Super Falcons ta matan Najeriya ta sha kashi a wasanta na farko a gasar kwallon mata na duniya da aka fara a Jamus.

Faransa ce ta doke Najeriya daci daya me ban haushi a wasan daya kayatar matuka.

Marie-Laure Delie ce ta zira kwallon daya baiwa Faransa damar iya kaiwa zagaye na gaba a rukunin daya kunshi mai masaukin baki wato Jamus da kuma Canada.

Najeriya ta taka rawar musamman wajen kare bayanta amma tayi katari da rashin sa'a.

Kocin Super Falcons Eucharia Uche ta ce bata fidda ran cewar kasar zata iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba ba.

Najeriya zata hadu da mai masaukin baki wato Jamus a wasanta na gaba sai kuma karawa da Canada a wasanta na karshe a rukunin A.