U21:Spain ta lashe gasar matasan Turai

spain
Image caption Spain ta kama Turai

Spain ta lashe gasar kwallon matasan Turai ta 'yan kasada shekaru ashirin da daya, bayan ta doke Switzerland daci biyu da nema a Denmark.

Ander Herrera da Thiago Alcantara sune suka ciwa Spain kwallayen da suka bata nasara a wasan.

Sannan 'yan wasan Swiss Pajtim Kasami da Timm Klose duk sun kai harin cin kwallo amma basu samu nasara ba.

'Yan wasa Spain da suka haskaka lokacin karawar sune Javi Martinez Thiago da kuma Juan Mata.