Arsenal na shirin sayarda Cesc Fabregas

fabregas
Image caption Cesc Fabregas

BBC ta fahimci cewar Arsenal na shirin sayarda Cesc Fabregas ga Barcelona idan har kulob din biyu suka amince akan faranshinsa.

Gunners dai sunki amince da tayin farko akan Kyaftin din, amma a yanzu zasu amince idan har aka kara kudi.

Babban jami'in Arsenal ya ce"sun yi mana tayi ta wajen shugabanmu Ivan Gazidis amma mun ce ba zamu yarda ba".

Da aka tambayeshi idan aka kara kudi zasu sayarda Cesc, sai yace"idan kudin yakai yadda muke so, zamu yarda".

A kakar wasan data wuce Arsenal taki amince da tayi har sau biyu daga Barcelona akan Fabregas.

A makon daya gabata shugaban Barcelona Sandro Rosell yace Fabregas na kokarin komawa kulob dinsa daya bari tun yana shekaru 16, amma dai Barca ba zata biya fiye da fan miliyan 35 akansa ba.

A halin yanzu dai Barcelona ta bada tayin kusan fan miliyan 27, amma dai Arsenal na tunanin akalla fan miliyan 40.