Wenger na kokarin shawokan Clichy ya zauna

clichy Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gael Clichy

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya bayyana cewar yanason Gael Clichy ya cigaba da taka leda a kulob din.

Kuma a halin yanzu Clichy ya soma tattaunawa da kocin akan batun.

Dan kwallon mai shekaru ashirin da biyar a kwannan nan ake ta alakantashi da wasu kulob din musamman Inter Milan a Italiya.

Har wa yau Bayern Munich da Liverpool da Manchester City da kuma Roma rahotanni sun nuna cewar suna zawarcin matashin dan kwallon.

Amma dai Wenger ya ce yana kokarin shawokan dan kwallon bayan don kada ya bar Emirates.

A kai'da sauran shekara guda kwangilar Clichy ta kare a Arsenal.