Ba zan bar United saboda Young ba-Nani

Nani
Image caption Dan kwallon Portugal Nani

Dan wasan Manchester United Nani ya ce yana maraba da zuwan Ashley Young a Old Trafford duk da cewar tsohon dan wasan Aston Villa din barazana ce gare shi.

Young mai shekaru 25 a makon daya gabata ne ya kulla yarjejeniyar fan miliyan 16 da zakarun kwallon Ingila kuma ana ganin cewar zai yi kokarin samun damar buga kwallo a zubin farko a cikin yaran Sir Alex Ferguson.

Young ya kasance na biyu a gasar premier wajen bada kwallo a zira a raga inda yake bayan dan Arsenal Cesc Fabregas.

A cewar Nani dai ba zai bar United ba kuma ze zauna yayi kokawar neman buga kwallo tsakaninshi da Ashley Young.

Nani yace"idan aka kawo sabbin 'yan wasa, abinda nada kyau ga kulob saboda karin 'yan wasa na taimakawa wajen lashe kofina".

Nani ya kara da cewar lokacin da Cristiano Ronaldo ke kulob din yayi kokari wajen nuna kwarewarsa.