Neymar baya son barin Brazil-Shugaban Santos

neymar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Neymar

Shugaban kungiyar Santos Luiz Alfaro de Oliveira Ribeiro ya bayyana cewar Neymar baya son ya bar kulob din.

Dan kwallon mai shekaru 19 ana ganinsa a matsayin matashin dan wasa a Kudancin Amurka mai tashe, kuma Real Madrid da Chelsea na zawarcinsa.

A cewar Ribeiro, Neymar na son zama dan kwallon da yafi kowanne a duniya don haka baya son yayi gaggawar ficewa daga Brazil.

Ya kara da cewar anata bada tayi mai tsoka, amma Neymar hankalinshi na waje guda.

Neymar da wasu 'yan wasan Santos Ganso da Elano a halin yanzu suna Argentina tare da babbar tawagar Brazil don fafatawa gasar Copa America.