River Plate ta fada rukuni na biyu

River Plate Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Wannan ne karo na farko da River Plate ta fadi a shekaru 110

Daya daga cikin manyan kulob-kulob a Kudancin Amurka River Plate, ta fadi daga rukunin farko na gasar League a Argentina a karon farko cikin shekaru 110.

River na bukatar ta lashe wasanta na karshe ne da kwallaye biyu domin ta kaucewa fadawa rukunin B na gasar kwallon ta Argentina.

Amma sai suka tashi 1-1 a wasan da suka fafata da Belgrano de Cordoba.

Wasan wanda aka buga a filin wasa na River Plate da ke birnin Buenos Aires, an tsaida shi ne a mintin karshe bayan da rikici ya barke a filin wasan.

'Yan sanda sun yi amfani da ruwa wajen tarwatsa magoya bayan River wadanda suka kutsa kai filin wasan a fusace.

Majiyar lafiya ta ce akalla mutane 25 ne suka samu raunuka.