Muna fargaba wajen buga wa Ingila - Carragher

Jamie Carragher
Image caption Jamie Carragher ya yi ritaya daga taka wa Ingila leda bara

Tsohon dan wasan Ingila Jamie Carragher ya bayyana cewa 'yan wasan Ingila kan samu fargaba a lokacin da suke taka wa kasar ta su leda.

"Idan ka yi kuskure daya, to shi kenan ka shiga-uku," kamar yadda dan wasan na Liverpool ya shaida wa BBC.

"A kulob dinka, kasan ba za a kusheka akai-akai ba, kuma bayan kwanaki uku za a sake wani wasan daban.

"Amma idan kana bugawa Ingila, sai ka shafe watanni ba a sake yin wani wasanba. Wannan ita ce damuwar da muke da ita idan muna buga wa Ingila."

Carragher, yana magana ne shekara guda bayan Ingila ta sha kashi a gasar cin kofin duniya, ya ce shi yasa 'yan wasan ke fargaba a gaban 'yan jarida.

"Matsawar da 'yan jarida ke yi na shafar 'yan wasa," a cewar dan wasan mai shekaru 33.

"Wani lokacin 'yan wasan kan gwammace 'yan jarida su yaba musu maimakon kocinsu."

Ingila ta sha kashi a hannun Jamus ne a gasar cin kofin duniya, inda Jamus din ta doketa da ci 4-1 a zagaye na biyu.