Ba ruwan Inter da abin kunyar Serie A

Ba ruwan Inter da abin kunyar Serie A
Image caption Massimo Moratti ya ce ba ruwan Inter da Calciopoli

Shugaban Inter Milan Massimo Moratti ya nanata cewa ba ruwan kulob din da abin kunyar da ya faru a gasar Serie A a 2006 wanda ake wa lakabi da Calciopoli.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Italiya (FIGC), ta zargi Juventus da hada baki da alkalan wasa domin zabar alkalan wasan da take so su jagoranci wasanta.

Kuma hakan ne yasa Hukumar ta kwace gasar Serie A din da Juventus ta lashe a shekara ta 2005 da 2006.

Sai dai a yanzu Juventus ta nemi a mayar mata da kofunan nata bayan da ta bayyana cewa a kwai kungiyoyi kamar 16 zuwa 20 da ke da hannu a abin kunyar da ya faru.

Nan da 'yan kwanaki ne ake saran yanke hukunci kan karar da Juventus ta daukaka, amma shugaban na Inter ya ce baya tsoron sakamakon.

"Ina da kwarin gwiwa ba mu da wata alaka da Calciopoli, kuma ina fatan gaskiya za ta sake yin halinta."

An kwace gasar Scudetto da Juventus ta lashe a shekara ta 2005 ba tare da an baiwa wani kulob ba, amma an kwace wanda ta lashe a 2006, sannan aka baiwa Inter Milan.