Fifa:Ivory Coast ta shiga gaban Ghana

fifa Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Shalkwatar Fifa a Switzerland

Ivory Coast ta shiga gaban Ghana a matsayin kasa ta farko a Afrika a fagen kwallon kafa a duniya, kamar yadda Fifa ta sanar.

A yanzu Ivory Coast kuma itace ta 14 a duniya a yayinda Ghana ta koma ta 33 a duniya amma ta biyu a Afrika. Masar ce ta uku a Afrika sai kuma Burkina Faso take matakin na hudu a yayinda Najeriya ke ta biyar a duniya amma kuma ta arba'in da daya a duniya.

Jerin goma na farko a Afrika:

1. Ivory Coast (14 a duniya) 2. Ghana (33 a duniya) 3. Masar (34 a duniya) 4. Burkina Faso (37 a duniya) 5. Najeriya (41 a duniya) 6. Senegal (43 a duniya) 7. Afrika ta Kudu (47 a duniya) 8. Kamaru (48 a duniya) 9. Algeria (51 a duniya) 10. Tunisia (57 a duniya)

Jerin manyan kasashen a duniya:

1. Spain 2. Netherlands 3. Jamus 4. Ingila 5. Brazil 6. Italiya 7. Portugal 8. Croatia 9. Mexico 10. Argentina