Zamu maida hankali wajen cin kwallaye-Villas-Boas

boas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andre Villas Boas

Sabon kocin Chelsea Andre Villas-Boas yayi alkawarin maida hankali wajen kai harin zira kwallo a cikin tawagarsa a Stamford Bridge.

Dan shekaru talatin da uku ya sanya hannu a kwangilar shekaru don maye gurbin Carlo Ancelotti.

Villas-Boas ya nada tsohon kocin West Brom Roberto Di Matteo a matsayin mataimakinsa.

Dan kasar Portugal din yace "ba wai samun galaba kadai ba, amma samun galaba tare da nuna kwarewa".

Ya kara da cewar"Na nada Roberto cikin wadanda zasu yi aiki dani, kuma mutum ne da yasan yadda wasan yake".

An kori Ancelotti a karshen kakar wasan data wuce shekara guda bayan ya jagoranci kulob din ya lashe kofina biyu.

Villas-Boas ya amince abinda ke gabansa shine lashe gasar premier ta Ingila ba tare da bata lokaci ba, a yayinda Blues zata buga wasanta na farko tsakaninta da Stoke a ranar 13 ga watan Agusta.