An zargi shugaban Birmingham da almundahana

Carson Yeung
Image caption Carson Yeung ya mallaki kashi 29.9 a Birmingham

Shugaban Birmingham City Carson Yeung ya gurfana a gaban wata kotu a kasar Hong Kong kan zargin halarta kudaden haram.

Kotun da ke Gabashin kasar - inda aka haifi Mr Yeung, ta bada belinsa bayan da aka tuhume shi da laifuka biyar.

Wakiliyar BBC Annemarie Evans ta ce jami'an da ke bincike kan harkokin kudi ne suka yi awangaba da shi a wani kasaitaccen gidansa.

Mr Yeung ya karbi ragamar kulob din ne, wanda ya fada gasar Championship a watan Mayu, a shekara ta 2009.

An dage sauraren karar har zuwa ranar 11 ga watan Agusta.

Ms Evans ta ce kudaden da ake zarginsa akai sun tasamma fan miliyan 59.

Ta ce Mr Yeung bai amsa ko kuma musanta laifin da aka zarge shi da aikatawa ba, kuma babu cikakkun bayanai kan zargin da ake masa.