Sunderland ta sayi Ji Dong daga Dragons

Ji Dong Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan Koriya ta Kudu Ji Dong-Won

Sunderland ta kamalla kulla yarjejeniyar da dan kwallon Koriya da Kudu Ji Dong-won daga kungiyar Chunnam Dragons.

Dan shekaru ashirin ya sanya hannu a kwangilar shekaru uku don murza leda a 'Stadium of Light'.

Dong-won ya zira kwallaye shida a karawa 11 da ya bugawa kasarsa, cikin hadda kwallaye hudu lokacin gasar cin kofin kasashen nahiyar Asiya.

Har wa yau, Ji yaci kwallaye 16 a fafatawa 44 a kungiyar Dragon dake yankin Gwangyang.

Shine dan kwallo na biyu da Sunderland ta siya cikin kwanaki biyu, bayan ta siyo Connor Wickham akan fan miliyan takwas.