Matakan FA akan United sunyi tsauri-Gill

gill
Image caption Sir Alex Ferguson da David Gill

Shugaban Manchester United David Gill yace babu makawa hukumar kwallon Ingila wato FA na daukar tsauraran matakai akan kulob din.

An dakatar da Wayne Rooney na wasanni biyu saboda kalaman da yayi a gaban Talabijin.

Shima kocin kulob din Sir Alex Ferguson an dakatar dashi na wasanni biyar saboda kalamansa akan alkalin wasa Martin Atkinson.

Gill yace" akwai hukunce hukuncen da watakila ba zasu shafi kowa ba, amma dai akwai tsauri a wasu hukuncin".

Ya kara da cewar"Ba wai nace kalaman Wayne sun yi dai dai ba, ko kuma na Sir Alex amma dai ina ganin cewar an yi haka ne saboda mu manya ne".

Gill a wani littafi daya rubuta akan United yayi tambaya akan cewar idan da wasu 'yan kwallo ne suka yi laifi irin na Rooney za a hukuntasu kuwa?