Dan Ivory Coast Meite ya koma Dijon a Faransa

meite
Image caption Abdoulaye Meite

Kungiyar Dijon ta Faransa wacce zata soma taka leda a matakin farko ya kulla yarjejeniya da dan kwallon Ivory Coast Abdoulaye Meite.

Dan wasan bayan ya sanya hannu a kwangilar shekaru uku.

Ya koma kungiyar ta Faransa ne bayan karewar kwangilarsa tare da West Bromwich Albion ta Ingila.

Kafin ya koma West Brom a shekara ta 2008, ya taka leda a Red Star Belgrade daga 1998 zuwa 2000), sai Marseille daga 2000-2006 da kuma Bolton Wanderers a 2006 zuwa 2008.

Meite ya bugawa Elephants din Ivory Coast wasanni 48.