Ina son Mourinho duk da kalamansa -Platini

platini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Uefa Michel Platini

Shugaban UEFA Michel Platini ya ce yanason kocin Real Madrid Jose Mourinho duk irin kalaman kocin akan cewar ana nuna bambamci, abinda ya haddasa aka dakatar dashi.

Platini a wata tattaunawa da jaridar La Marca ya ce"Ina bashi mahimmanci, Ina son Mourinho".

Real Madrid na kalubalantar dakatarwar wasanni uku da aka yiwa Mourinho bayan Real ta sha kashi a wajen Barcelona a wasan zagayen kusada karshe na gasar zakarun Turai.

A ranar 29 ga watan Yuli za a saurari daukaka karar da Real keyi akan kocinta mai shekaru 48.

Bayaga dakatarwar, anci tarar Mourinho dala dubu saba'in da biyu.

Daga bisani dai Barcelona ta samu galaba akan Real a Santiago Bernabeu daci biyu da nema, sai kuma suka tashi kunen doki a Nou Camp, kafin Barca din ta lashe gasar bayan ta doke Manchester United a wasan karshe.