Tennis: Sharapova ta tsallake zuwa wasan karshe

sharapova
Image caption Maria Sharapova

Maria Sharapova ta tsallake zuwa wasan karshe na gasar Wimbledon a karon farko tun shekara ta 2004 bayan ta lallasa Sabine Lisicki a wasan zagayen kusada karshe.

'Yar kasar Rashar wacce itace ta biyar a tennis na duniya a bangaren mata ta doke Lisicki da seti biyu a jere.

Sharapova a yanzu zata hadu da Petra Kvitova a ranar Asabar a wasan karshe.

Ita dai Petra Kvitova ta samu gurbin zuwa wasan karshen ne bayan ta samu galaba akan Victoria Azarenka.

Wannan ne karon farko da Kvitova zata buga wasan karshe na babbar gasa a tennis wato 'Grand Slam'.

A bara dai Kvitova ta sha kashi a wasan karshe a hannun Serena Williams.