Vincent Enyeama ya koma Lille

Vincent Enyeama
Image caption Enyeama yana haskakawa sosai a 'yan shekarun nan

Golan Super Eagles na Najeriya Vincent Enyeama ya koma zakarun gasar kwallon Faransa na bana Lille daga Hapoel Tel Aviv na Isra'ila.

Dan wasan ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru uku kan farashin da ba a bayyana ba.

Enyeama mai shekaru 28 ya ce ya yi maraba da damar da ya samu ta taka leda a gasar kwallon Faransa.

"Abu ne mai kyau kasancewa anan da kuma taka leda a gasa mai tsauri kamar ta Faransa," kamar yadda Enyeama ya shaida wa BBC.

"Wannan ba karamar dama bace. Na samu nutsuwa tun kafin na isa can - kuma wannan ba karamar nasara bace.

A yanzu Enyeama zai samu damar taka leda a gasar zakarun Turai ganin cewa Lille ta lashe gasar kwallon Faransa.

Bayan da ya yi watsi da damar da ya samu daga kungiyoyi a Ingila da Spain da Portugal, dan wasan na Najeriya yana fatan matakin da ya dauka zai zamo mafi dacewa a gare shi.