Dan Zimbabwe Musona zai koma Hoffenheim

 Knowledge Musona Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Musona yana taka rawa sosai a gasar Afrika ta Kudu

Dan wasan Zimbabwe Knowledge Musona zai tafi Jamus ranar Litinin domin tattaunawa kan yiwuwar komawarsa Hoffenheim.

Kulob din na gasar Bundesliga ya samu amincewar kulob din dan wasan wato Kaizer Chiefs kan farashin da suka taya shi.

Shi ne dan wasan da ya fi kowanne zira kwallaye a gasar Afrika ta Kudu da kwallo 15 a bara, kuma a 'yan kwanakin nan an danganta shi da kulob din Celtic na Scotland.

"Mun cimma matsaya tsakanin kulob da kulob, a yanzu ya rage tsakanin su da dan wasan kan ababen da yake so," a cewar manajan Kaizer Chief Bobby Motaung.

"Ba magana bace ta gwaji, za mu je can ne domin tattaunawa kan kwantiragi da kuma gwajin lafiya, kuma daga nan ne dan wasan zai gani idan kulob din ya yi masa.

"Daga baya sai mu yanke hukunci daga can."

Dan wasan ya ja hankali ne bayan da ya zira kwallaye biyu a wasan da Zimbabwe ta doke Mali 2-1 a wasan share fage na shiga gasar cin kofin kasashen Afrika da za a yi a 2012.