Kwamitin Majalisar Burtaniya ya soki FIFA

Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Fifa Sepp Blatter na fuskantar matsin lamba

BBC ta fahimci cewa kwamitin bincike na Majalisar Dokokin Burtaniya ya nemi Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta gudanar da cikakken bincike a kan zargin da ya mamayeta na cin hanci da rashawa. An zargi Hukumar ta FIFA bisa yadda ta bayar da damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2022. An kuma soki FIFA a kan yadda ta bullowa batun cin hanci a babban taronta wanda aka gudanar a watan da ya gabata.

Za a gabatar da rahoton binciken kwamitin na al'adu da wasanni da kuma harkokin yada labarai a ranar 5 ga watan Yuli.

BBC ta fahimci cewa rahoton zai soki yadda FIFA ta nuna "halin ko in kula" ga hujjojin da jaridar Sunday Times ta gabatar wanda ya zargi jami'anta biyu, Amos Adamu da Reynald Temarii, da neman karbar rashawa domin zaben Qatar ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2022.

Daga bisani an dakatar da mutanen daga shiga harkokin kwallon kafa na tsawon shekaru uku da kuma shekara daya daki-daki.

Sai dai kwamitin da'a na FIFA ya yi watsi da batun hadin baki tsakanin kasashen Spain da Portugal wadanda ke neman bakuncin gasar a 2018, da Qatar wacce ke neman ta 2022.

Baya ga zargin FIFA, rahoton kwamitin Majalisar zai kuma yi kira ga hukumar da ta sake nazari na cikin gida a kan yadda Ingila ta kasa samun damar daukar bakuncin gasar a shekara ta 2018.

Ingila dai ta sha kunya a zaben da aka gudanar, inda ta samu kuri'u biyu kacal sannan aka fitar da ita a zagayen farko.

Duk da cewa Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA, ta fara gudanar da bincike na mako biyu a kan zargin tsohon mataimakin shugaban FIFA Jack Warner da Lord Triesman ya yi, ba ta binciki yadda bukatar ta Ingila ta kasance ba.