Tennis:Djokovic ya doke Nadal a wasan karshe

djokovic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Novak Djokovic ya doke Nadal

Dan kasar Serbia Novak Djokovic ya lashe gasar Wimbledon a karon farko a tarihinsa bayan ya samu galaba akan Rafael Nadal a wasan karshe.

Djokovic ya samu nasara a seti uku a yayinda Nadal ya samu seti daya, kuma a yanzu Djokovic ya zama na farko a fagen tennis a duniya.

Wannan ne nasara ta biyar da Djokovic ya samu akan Nadal a bana sannan kuma ya samu nasara a wasanni 50 cikin 51 daya fafata.

Ya kasance dan kasar Serbia na farko daya lashe kofin Wimbledon, sannan babbar gasa ta uku kenan daya lashe bayan lashe Australian Open sau biyu.