Tennis:Kvitova ta lashe Wimbledon Open

Petra Kvitova Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Petra Kvitova ta lashe gasar Wimbledon open

Petra Kvitova ta lashe gasar Wimbledon open ta tennis bayan ta doke Maria Sharapova a wasan karshe a ranar Asabar.

A bara Serena Williams ce ta fidda Kvitova a gasar, amma a bana ta casa Sharapova don lashe babbar gasa ta farko a tarihinta na buga tennis.

'Yar kasar Czech,Kvitova mai shekaru 21 tace" a bara na samu gogewar buga zagayen kusada karshe, sai nace a yanzu zan iya lashe gasar".

'Yar Rasha Maria Sharapova mai shekaru 24 wacce ta taba lashe gasar a shekara ta 2004 ta jinjinawa Kvitova.

Kvitova wacce ke bugu da hannu hagi ta samu galaba ne da seti biyu a jere wato 6-3, 6-4.