Clichy ya kulla yarjejeniya da Man City

clichy Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gael Clichy

Dan kwallon Arsenal Gael Clichy ya sanya hannu a yarjejeniyar shekaru hudu da Manchester City.

Dan kwallon mai shekaru 25 ya koma Eastlands akan fan miliyan bakwai.

Clichy ya koma Gunners ne daga kungiyar Cannes ta Faransa a shekara ta 2003 kuma kwangilarsa a Emirates zata kare a bara.

Clichy a watan daya wuce ne ya bayyanawa Arsenal cewar yanason barin kulob din.

A halin yanzu kocin Arsenal Arsene Wenger na cikin mawuyacin hali saboda kyaftin dinsa Cesc Fabregas na kan hanyarsa zuwa Barcelona

Sannan kuma Sami Nasri shima yana da alamun barin kulob din inda aka tunanin City ne ko Manchester United.