Nayi kura kurai a rayuwata-In ji Cole

cole Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ashley Cole

Dan kwallon Chelsea da Ingila Ashley Cole ya ce kada mutane su dubeshi akan yadda yake tafiyar da rayuwarsa amma su lura da irin yadda yake murza leda.

Cole wanda yasha suka a jaridu, ya shaidawa BBC cewar"Na yi wasu kura kurai kuma babu yadda mutane zasu manta".

Ya kara da cewar"Ku yanke mani hukunci akan yadda nake buga kwallo ko kuma yadda ganawarmu ta kasance gaba da gaba".

Kalamansa na zuwa ne jim kadan bayan sabon kocin Chelsea Andre Villas-Boas ya ce yanason 'yan wasansa su zama jakadu nagari.

An gargadi Cole bisa dabi'unsa a bana lokacin daya harbi wani dalibi bisa kuskure.

Har wa yau dan kwallon Ingila mai shekaru 30 ya rabu da matarsa wato shahararriyar mawakiya Cheryl a bara.

A farkon rayuwarsa ta kwallo, an ci tarar Cole fan dubu 100 lokacin daya tattauna da Chelsea cikin sirri duk da cewar kwangilarsa a Arsenal bata kare ba.