NFF ta nemi bayanai akan tsare Emmenike a Turkiya

emenike
Image caption Emmanuel Emenike

Hukumar kwallon Najeriya NFF ta bukaci hukumomi a kasar Turkiya su bata cikakken bayani akan dilalan tsaren dan kwallon kasar Emmanuel Emenike.

Emmenike na daga cikin mutane kusan hamsin da 'yan sanda suka damke bisa zargin hadin baki wajen sayarda wasa da kuma joge har ya kaiga Fenerbahce ta lashe gasar kwallon kasar.

Wata jaridar Turkiya ta zargi Emenike wanda a lokacin yake bugawa kulob din Karabukspor da kuma wani dan wasa Sezer Ozturk cewar a karawar kungiyoyinsu da Fenerbahce kada su taka rawar gani don bayan kamalla gasar sai su kuma Fenerbahce.

Daga bisani dai bayan kamalla gasar Emenike ya koma Fenerbahce daga Karabukspor akan dala miliyon tara.

Wasu daga cikin wadanda aka tsaren sun hada da attajirin dan kasuwa kuma shugaban Fernebache Aziz Yildrim.

Fenerbache ta fitar da sanarwar karyata ba dai dai ba.