Real Madrid ta sayi Coentrao daga Benfica

Coentrao Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fabio Coentrao

Real Madrid ta sayi dan kwallon Benfica Fabio Coentrao akan Euro miliyon talatin.

Real Madrid ta sanarda cewar dan kwallon ya kulla yarjejeniyar shekaru shida da ita.

A yau ne aka gwada lafiyarsa, sannan ya rattaba hannu a kwangilar.

Dan kwallon Portugal din mai shekaru 23 ana saran kwangilar shekaru biyar zai kulla da Real don aiki karkashin Jose Mourinho.

Coentrao na cikin tawagar Benfica data lashe kofina biyu a shekara ta 2009 kuma ya bugawa Portugal kwallo a gasar cin kofin duniya a shekara ta 2010.

Shine dan kwallo na biyar da Mourinho ya siya don shiryawa kakar wasa nai zuwa.

'Yan kwallon baya mafi tsada a duniya:

1 - Rio Ferdinand £29.1m (Daga Leeds United zuwa Manchester United, 2002)

2 - Fabio Coentrao £27m (Daga Benfica zuwa Real Madrid, 2011)

3 - Pepe £25m (Daga Porto zuwa Real Madrid, 2007)

4 - Daniel Alves £23.5m (Daga Sevilla zuwa Barcelona, 2008)

5 - Dmytro Chygrynskiy £22.5m (Daga Shakhtar Donetsk zuwa Barcelona, 2009)

=6 - Joleon Lescott £22m (Daga Everton zuwa Manchester City, 2009)

=6 - Lilian Thuram £22m (Daga Parma zuwa Juventus, 2001)

8 - David Luiz £21.3 (Daga Benfica zuwa Chelsea, 2011)

9 - Alessandro Nesta £21m (Daga Lazio zuwa AC Milan, 2002)

10 - Ricardo Carvalho £20m (Daga Porto zuwa Chelsea, 2004)