Gerrard ba zai bi Liverpool rangadi ba

gerrard Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Steven Gerrard

Steven Gerrard ba zai shiga cikin rangadin da Liverpool zata yi a nahiyar Asiya ba sakamakon jinyar tiyatar da aka yi masa.

Dan kwallon mai shekaru 31 ya shafe kusan watanni hudu bai taka leda ba.

Kocin Liverpool Kenny Dalglish ya bayyana cewar"Steven da likitocinmu na kokarin ganin ya warware".

Ya kara da cewar"Na san cewar mutane zasu so ganin Steven ya buga wasanmu na bude gasar tsakaninmu da Sunderland".

Gerrard dai an yi masa tiyata sakamakon raunin daya samu a wasansu da Chelsea a watan Fabarairu.

Amma sai yayi katari da rashin sa'a abinda ya haddasa aka kara masa tiyata a watan Afrilu.

Liverpool zata buga wasanni a China da Malasyia sannan tayi horo a Singapore a rangadin kwanaki takwas da zata fara a ranar Lahadi.

Zata buga wasanta na farko a gasar premier a gida tsakaninta da Sunderland a ranar 13 ga watan Agusta kafin ta tafi gidan Arsenal a makon gaba.