Ina so na bar Manchester City - Carlos Tevez

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dangantaka tsakanin Tevez da Mancini ta yi tsami a baya-bayan nan

Dan wasan Manchester City Carlos Tevez ya fitar da wata sanarwa inda ya ce yana son barin kulob din saboda wasu dalilai da su ka shafi iyalinsa.

Dan wasan na kasar Argentina ya taimaka wa City ta kare a mataki na uku a gasar Premier da aka kammala a kakar da ta gabata, sannan ta samu damar zuwa gasar zakarun Turai.

Tavez mai shekaru 27, wanda ya zo City daga United, ya ce ba zai iya ci gaba da zama a garin Manchester ba tare da 'ya'yansa ba.

"Ina so na kasance a kusa da su, kuma na shafe lokaci mai tsawo tare da su," a cewar Tavez a wata sanarwa.

"Zama ba tare da 'ya'yana ba a Manchester yana sani cikin damuwa. Komai na ke yi a duniyar nan ina yinsa ne saboda su.

"Ina bukatar su kasance cikin farin ciki saboda na mika rayuwata a gare su.

"Ina fatan mutane za su gane halin kuncin da na shiga a watanni 12 da suka gabata, dangane da iyali na."

Tevez ya taka rawar gani a City, inda ya zira kwallaye 29 a wasanni 42, a shekararsa ta farko, sai dai ba su je gasar zakarun Turai ba.

Daga baya an baiwa dan wasan mukamin kyaftin, inda kuma ya zira kwallaye 24 a wasanni 44 da ya taka, inda ya taimakawa kulob din ya kai gasar zakarun Turai.

Tevez ya kuma lashe kofin FA bayan da suka lashe Stoke da ci 1-0 a watan Mayu - kofi na farko da City ta lashe a shekaru 35.

Sai dai dangantaka tsakaninsa da koci Mancini ta yi tsami lokacin da ya mika bukatar barin kulob din a watan Disamban 2010, wacce daga baya ya janye.