Liverpool ta sasanta da Blackpool akan Adam

adan
Image caption Charlie Adam

Liverpool ta kamalla yarjejeniya da Blackpool akan sayen dan kwallon Scotland Charlie Adam.

Adam mai shekaru 25 zai tafi Merseyside don a gwada lafiyarsa kuma su sasanta akan cinikin.

A watan Janairu Liverpool ta taya Adam sau biyu akan fan miliyon shida da rabi amma Blackpool taki amince, sai dai a yanzu rahotanni sunce cinikin zai kai fan miliyon tara.

Adam ya koma Blackpool ne daga kungiyar Rangers akan fan dubu dari biyar a shekara ta 2009.

Idan ya koma Liverpool zai kasance dan kwallo na biyu da Kenny Dalglish ya siya bayan Jordan Henderson daga Sunderland akan fan miliyon ashirin.

Har wa yau rahotanni sun nuna cewar golan Roma dan kasar Brazil Alexander Doni na kan haryarsa ta koma Liverpool.

Sannan kuma Aston Villa taki amincewa da tayin fan miliyon 15 akan Stewart Downing da Liverpool ta mika mata a ranar Talata.