City ta sayi Savic daga Partizan Belgrade

Stefan Savic Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Stefan Savic

Dan kwallon Montenegro Stefan Savic ya kulla yarjejeniya da Manchester City daga Partizan Belgrade.

Dan wasan mai shekaru 20, ya kasance dan kwallon baya na biyu da City ta siyo a kasuwar musayar 'yan kwallon bayan Gael Clichy daga Arsenal.

Savic ya sanya hannu a kwangilar shekaru hudu tare da City.

Yace"Na dade ina kallon gasar premier kuma na fahimci cewar wajen zuwa ne kuma na shirya taimakawa kulob din don samun nasara".

Savic ya kara da cewar"buri na ya cika, zan hadu da Edin Dzeko da Aleksandar Kolarov wadanda muke harshe guda dasu".

A baya dai Arsenal ta gayyaci Savic a matsayon gwaji amma sai basu sasanta ba.