United ta bada tayin fan miliyon 20 akan Nasri

nasri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samir Nasri

Manchester United ta ce tana saran sayen Samir Nasri duk da cewar Arsenal ta ce ba a gabatar mata da bukatar sayen dan kwallon Faransan a rubuce ba.

BBC ta tabbatar da cewar United ta bada tayin fan miliyon 20 akan dan kwallon mai shekaru 24 a makwannin da suka wuce.

Arsenal ta ce babu alamun dake nuna bukatar sayen dan kwallon sai dai kawai an nuna sha'awa ne.

Nasri yaki sabunta kwangilarsa a Arsenal wacce sauran shekara guda ta kare.

Ana saran zai tattauna da Arsene Wenger cikin sa'o'i ashirin da hudu masu zuwa.

Har wa yau Wenger na cikin damuwar watakila ya rabu da kyaftin dinsa Cesc Fabregas zuwa Barcelona bayan ya sayarda Gael Clichy zuwa Manchester City a ranar Litinin.

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson yana kokarin karawa tawagarsa karfi ne saboda ritayar da Paul Scholes da kuma Ryan Giggs.