Liverpool ta sayi Charlie Adam

Image caption Charlie Adam

Liverpool ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar Blackpool, Charlie Adam.

Dan wasan mai shaikarun haihuwa, 25, ya rataba hannu ne a kwantaragi a ranar alhamis bayan an gama duba lafiyarsa.

"Ina matukar farin ciki da komawa Liverpool," In ji Adam.

"Gaskiya al'amarin ya dau tsawon lokaci. Abun da nake jira yanzu shine kawai in fara taka leda a kungiyar domin nuna kwarewa ta."

Ya kara da cewa: "Liverpool babbar kungiya ce da take da manyan 'yan wasa da kuma masu horadda kungfiyar."