Smalling ya samu sabon kwantaragi a Man U

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chris Smalling

Dan wasan bayan Manchester United, Chris Smalling ya sa hannu a sabon kwantaragi na tsawon shekaru biyar a kungiyar.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 21 ya baro Fulham ne a bara kuma ya takwa United leda sau 16 a wasanni a kakar wasan bara wanda Manchester United ta lashe.

Dan wasan ya shaidawa shafin intanet din kungiyar cewa: "Wannan babbar kungiya ce, kuma a dan lokacin dana zo kungiyar na samu nasarori.

Sabon kwantaragin da Smalling ya sa hannu zao sa ya takawa United leda har zuwa shekarar 2015.