Almunia da Bendtner na shirin barin Arsenal

bendner da almunia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bendner da Almunia

Golan Arsenal Manuel Almunia da dan kwallon gaba Nicklas Bendtner na tattaunawa don barin Emirates zuwa wani kulob din.

Bendtner mai shekaru 23 da Almunia mai shekaru 34 basa cikin tawagar 'yan kwallo 23 na Arsenal wadanda zasu tafi rangadi zuwa nahiyar Asiya.

Kakakin Arsenal ya tabbatar da cewa 'yan wasan biyu suna tattaunawa da canza sheka.

Kocin Gunners Arsene Wenger ana saran ya bada bayanai dalla-dalla akan batun musayar 'yan kwallon a ranar Litinin.

Kyaftin din Arsenal Cesc Fabregas ana alakantashi da komawa Barcelona this summer kuma ba zai shiga cikin rangadin ba saboda rauni.

Sai dai Samir Nasri wanda Manchester United ke zawarci zai tafi rangadin da sauran 'yan tawagar.

Dan kasar Spain Almunia ya koma Arsenal ne daga Celta Vigo a shekara ta 2004 a yayinda shi kuma dan kasar Denmark Bendtner ya hade da Arsenal a shekara ta 2005.