Real Madrid zata danne Barca a karkashin Mourinho-Beckham

Beckham Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan wasa LA Galaxy David Beckham

Real Madrid na kan hanyar lashe komai a duniya a karkashin Jose Mourinho kamar yadda tsohon dan wasa a Santiago Bernabeu David Beckham yayi hasashe.

Tsohon kyaftin din Ingila wanda ya shafe shekaru hudu a Real daga shekara ta 2003 zuwa 2007, ya ce kocin dan kasar Portugal zai bada mamaki a kakar wasa mai zuwa kuma zai kawo karshen kaka gidan Barcelona a gasar La Liga.

Beckham ya shaida jaridar Marca: "Madrid nada karfin gaske da manyan 'yan wasa, ina ganin zata lashe duka gasa kuma suna da kocin daya kware".

Dan wasan Los Angeles Galaxy ya kuma jinjinawa tsohon dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo wanda ya bayyana a matsayin kashin bayan cigaba Real Madrid a wannan lokacin.