Phillips ya koma Blackpool daga Birmingham

Kevin Phillips Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kevin Phillips

Dan Ingila Kevin Phillips ya koma Blackpool daga kungiyar Birmingham City.

Dan wasan mai shekaru 37 ya amince da yarjejeniyar shekara guda da kulob din tare da yiwuwar sabunta kwangilar na karin watanni 12.

Phillips ya zira kwallaye 254 cikin wasanni 561 daya bugawa kulob daban daban guda bakwai sannan ya takawa Ingila leda sau takwas.

Phillips yace"Naci kwallaye da dama a rayuwata kuma ina ganin zan kara zira wasu".

Phillips ya bugawa Birmingham wasanni 20 a kakar wasan data wuce inda ya zira kwallaye hudu kafin kulob din ya bar gasar premier ya koma gasar Championship.

Ya fara taka leda a Baldock Town sannan ya koma Watford, Sunderland, Southampton, Aston Villa and West Brom kafin ya koma Birmingham.

Shine dan kwallo na uku da Blackpool ta siya a kwannan nan bayan Bojan Djordjic da kuma Matt Hill.