Danny Shittu ya sabunta kwangilarsa a QPR

shittu
Image caption Danny Shittu

Danny Shittu ya kulla yarjejeniyar karin shekara guda da kungiyar Queens Park Rangers ta Ingila.

Dan kwallon mai shekaru talatin a baya ya bugawa Rangers wasanni 174.

Shittu ya bugawa Najeriya wasanni 28 kuma ya taba taka leda a Watford da kuma Bolton Wanderers.

Ya shaidawa shafin Intanet na kungiyar Queens Park Rangers cewar" Naji dadin warwaren batun makomata kuma zan kara shekara guda tare da QPR".

Shittu ya kara da cewar"Na samu wasu damar a wadansu wuraren amma na fison wannan kulob din don in taimaka mata cigaba da kasancewa a gasar premier".