Essien na Ghana zai yi jinyar watanni shida

essen
Image caption Micheal Essien

Dan kwallon Chelsea Michael Essien zai shafe watanni shida yana jinya, bayan tiyatar da aka yi mashi a gwiwarsa.

Dan Ghana mai shekaru 28, ya jimu ne lokacin horon shiryawa kakar wasa mai zuwa.

Kocin Chelsea manager Andre Villas-Boas ya ce "Dukanmu na yiwa Micheal fatar warkewa cikin gaggawa".

Essien a shekara ta 2008 ma ya yi jinya ta watanni shida sakamakon raunin da yaji.

Rauni a gwiwarsa ya janyo bai buga gasar cin kofin duniya ba a shekara ta 2010.

Essien ya hade da Blues daga Lyon a shekara ta 2005 akan fan miliyon 24.4 kuma ya kasance babban dan kwallo a Stamford bridge.