Tottenham ta karya yarjejeniya- Modric

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luka Modric

Tottenham tayi tsayin daka na kin sayar da dan wasan ta Luka Modric duk da dan wasan ya yi korafin cewa kungiyar ta karya yarjejeniyar da ta dauka na barin sa ya tafi idan wata babbar kungiya ta zo neman sa.

Dan wasan dai ya zargin Shugaban kungiyar ne Daniel Levy da kin sayar da shi bayan kungiyar Chelsea ta taya shi akan fam miliyan 22.

Kungiyar Spurs dai ta ce babu wata yarjejeniya da ta kulla da dan wasan na barin ya tafi.

Modric ya ce: "A kakar wasan bara Levi ya shaida min cewa idan wata babbar kungiya ta zo nema na, kuma sun amince da kudin za su bari in tafi.

"Ina fata dai nan ba da dadewa ba, zamu san idan muka fuskanta."

Har yanzu dai Chelsea na nuna bukatar siyan Modric musamman ganin cewa dan wasanta Michael Essien ya samu rauni a gwiwarsa.