An warware takaddama tsakanin Siaisia da Osaze

osaez
Image caption Osaze Odemwingie

Hukumar kwallon Najeriya NFF ta sanarda cewa an warware rashin jituwar dake tsakanin kocin Super Eagles Samson Siasia da Osaze Odemwingie.

An samu takun saka ne tsakanin kocin da dan kwallon bayan da Siasia ya zargi Odemwingie akan cewar ya fice daga sansanin horon Super Eagles ba tare da bayyana inda zashi ba.

Sakamakon abinda Siasia ya kira rashin da'a, ba a gayyaci Osaze ba a wasan sada zumunci tsakanin Argentina da Najeriya da kuma wasan Super Eagles da Ethiopia na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika da za ayi a badi.

Amma a yanzu NFF ta ce matsakar ta kare kuma akwai yiwuwar gayyatar Osaze a wasan sada zumunci tsakanin Super Eagles da Black Stars na Ghana.

Jami'in NFF Barrister Chris Green yace"tsakanin Siasia da Osaze abin ya zama tarihi".