AAG 2011:Ghana na rukuni guda da Kamaru

maputo
Image caption A Moputo za ayi gasar wasanni Afrika

An rarraba kasashe zuwa rukuni rukuni bisa yadda zasu kara da juna a gasar kwallo na wasanni kasashen Afrika wato 'All Africa Games'.

A rukunin farko akwai Afrika ta Kudu da Mozambique da Libya da kuma Madagascar.

Sai rukuni na biyu daya kunshi kasar dake kokarin kare kofinta wato Kamaru da Ghana da Uganda da kuma Senegal.

Za ayi gasar wasanni Afrika ne daga ranar uku zuwa goma sha takwas ga watan Satumba a Maputo babban birnin Mozambique.