Hamburg na zawarcin Bendtner daga Arsenal

bendtner
Image caption Nichlas Bendtner

Darektan wasannin kungiyar Hamburg Frank Arnesen ya bayyana cewar kulon din na kokarin kulla yarjejeniya da dan kwallon Arsenal Nicklas Bendtner.

Bendtner mai shekaru 23 bai shiga tawagar Gunners data tafi rangadi yankin nahiyar Asiya, kuma Arnesen ya ce Hamburg na sha'awarsa sauran kadan a kamalla yarjejeniyar.

Arnesen yace"Bendtner zai dawo wajenmu".

Bendtner kuma an alakantashi da zakarun Bundesliga wato Borussia Dortmund amma dai Dortmund din ta nisanta kanta da dan kwallon Denmark din.