Da kamar wuya Nasri ya zo Man U- Ferguson

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samir Nasri

Sir Alex Ferguson ya ce Samir Nasri ya amince zai bar Arsenal amma da wuya dan wasan ya dawo Manchester United.

Rahotanni sun ce dai Manchester United na zawarcin dan wasan mai shekarun haihuwa 24, inda har ma su ka tayashi akan fam miliyan 20, amma Arsenal din taki amincewa.

"Bana ganin zai zo United," In ji Ferguson.

"Abun da zan iya gaya muku kenan, ina ganin ya amince zai zarce wata kungiyar."

Ganin cewa Paul Scholes ya yi murabus daga kwallon kafa a watan Mayu, Ferguson na kokarin neman wanda zai maye gurbinsa.