Corinthians ta bada tayin fan miliyon 35 akan Tevez

tevez
Image caption Carlos Tevez

Manchester City ta samu tayin fan miliyon 35 daga wajen kungiyar Corinthians ta Brazil akan Carlos Tevez amma akwai yiwuwar shugabanin City ba zasu yarda ba.

Corinthians na saran dan kwallon mai shekaru 27 zai koma kulob din inda ya samu nasarori daga shekara ta 2004-2006.

City na tunanin akan tayin Euro miliyon 40 din, amma da wasu bayanai na nuna cewar dole ne sai Corinthians sun kara wani abu akan Tevez din kafin su bada shi.

BBC ta fahimci cewar City a yanzu ta matse kaimi wajen zawarcin Sergio Aguero daga Atletico Madrid.

Ita dai Atletico ta nemi fan miliyon 45 akan Aguero kuma kudin da City ta karba daga wajen Tevez zai isa a siyo shi.