Fulham ta sayi Riise daga AS Roma

John Arne Riise Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption John Arne Riise

Fulham ta sayi tsohon dan kwallon Liverpool John Arne Riise daga AS Roma.

Dan wasan mai shekaru talatin ya amince da kwangilar shekaru don taka leda a Craven Cottage.

Riise yace"Na san kulob din na kokarin samun nasara a kowacce shekara".

Kocin Fulham Martin Jol ya bayyana Riise a matsayin gogaggen dan kwallo wanda zai karawa tawagar karfi.

John Arne Riise ya hade da kaninsa Bjorn Helge Riise a Fulham.

John Arne ya shafe shekaru bakwai a Liverpool inda ya buga wasanni 371 yaci kwallaye 34 kafin ya koma AS Roma a shekara ta 2008.