Hassan Shehata ya zama kocin Zamalek

Image caption Hassan Shehata

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Masar, Hassan Shehata ya zama sabon kocin kungiyar Zamalek ta kasar Masar.

Ya sami wannan aiki ne a dai dai lokacin da kungiyar Zamalek ta kori tsohon kocin ta wato Hossam Hassan bayada da kungiyar ta kasance na biyu a teburin wasanni, inda abokiyar hamaiyar ta Al-Ahly ta kasance zakara.

Shahata dai ya ajiye aikin sa ne bayanda tawagar kasar Masar ta yi kunne doki da takwarar ta ta kasar Afirka ta Kudu a wassan share fage na zuwa gasar cin kofin Afrika ta shekara ta 2012.

Wannan shawarar dai da kungiyar ta yanke na korar Hossam Hassan ba ta yi wa magoya bayan ta dadi ba.

Daya daga cikin 'yan kungiyar magoya bayan Zamalek din wanda aka fi sani da White Knight Ultra ya zargi hukumar gudanarwar kungiyar da rashin godiyar Allah, a cewar sa Hossam Hassan ya taka rawar gani wajen dawowa da martabar kungiyar ayayin da kungiyar take na goma sha'uku a teburin wasanni zuwa na biyu a gasar.

Magoya bayan dai na shirye shiryen gudanar zanga zanga a gaban hedkwatar kungiyar, don nuna rashin amincewar su da daukar Shahata aiki.

Kwangilar dai na nuni da cewa Hassan Shehata zai rika tashi da dalar Amurka dubu arba'in da biyu a kowani wata.