'Wesley Sneijder ba za shi ko'ina ba'

Image caption Wesley Sneijder

Darektan wasanni na kungiyar Inter Milan ta kasar Italiya Marco Branca ya tsaya kai da fata cewa kungiyar bata samu wani tayi a hukumance na saida Wesley Sneijder ba.

A baya bayan nan dai rahotanni sun shaida cewa kungiyar Manchester United na zawarcin dan wasan mai shekarun haihuwa 27 amma kungiyar Inter Milan ta jajirce kan tsayawar sa a kungiyar.

Mista Branca dai ya shaida cewa har wa yau basu sami wani tayi a hukumance ba, kuma basu da niyar sauraron hakan.

Da BBC ta tambaye shi ko shin akwai karin bayani kan lamarin sai ya ce ai Sneijder ba na sayarwa bane.

A farkon watan Yunin da ya gabata dai Sneijder ya shaida wa shafin Internet na Inter Milan cewa yana jin dadin zama a kungiyar kuma bai ga dalilin da zai sa ya bar kungiyar ba.

Rahotanni dai na nuni da cewa kungiyar Manchester United na gab da cimma yarjejeniyar sayan dan wasan a kan kudi fam miliyan talatin da biyar don zuwa taka tamoula a Old Traford.

Mista Branca ya jajirce wajen nanata cewar har wayau ba wani tayi a hukumance, kuma duk jitajita ne, ya kuma musanta cewar an shirya zama tsakanin wakilin Sneijder da kungiyar Inter Milan a wannan makon.